Masana harakokin diplomasiya na kasa da kasa na nan suna ta kokarin fahimtar wani sako da aka sato daga taskar sakkonin email na ‘yar takaran shugabar kasa a zaben bana a nan Amurka Hilary Clinton, wanda ke nuna kamar tana zargin gwamnatocin kasar Saudi Arabia da Qatar da laifin bada goyon baya na kayan aiki da mankurdan kudade ga mayakan ‘yantawaye na IS.
WASHINGTON, DC —
Wannan sakon daya ne daga cikin dubban sakkonin email na madugun kyamfen dinta John Podesta da aka sata kuma cibiyar tonon silili ta Wikileaks ta bankado su bainar jama’a.
Wani bangare na sakon yana cewa ne: “akwai bukatar muyi anfani da karfinmu na diplomasiya da leken assirrai wajen matsawa gwamnatocin Saudi Arabia da Qatar lamba da su daina bada taimakon da suke bayarwa a asirce na kudade da kayan aiki don tallafawa ISIL da na kungiyoyin ‘yan Sunni.”
Duk da cewa an dade ana zaton cewa Saudi Arabia da wasu kasashen Larabawa kawayen Amurka sun jima suna taimakawa wadanan kungiyoyin na ‘yan ta’adda da kudade, wannan zargin da aka gani a cikin sakon shine na farko da ya fito fili yana bayyana wannan tuhumar.