Dakarun da ke biyayya ga Shugaban Libiya Muammar Gaddafi sun yi luguden wuta kan inda sojojin ‘yan tawaye su ka ja daga a kusa da birnin Adjabiyya na gabashin kasar.
Jami’an asibiti da ‘yan tawayen sun ce an hallaka a kalla mutane 6 sannan 16 su ka sami rauni a wannan harin da aka kai jiya Asabar.
An fafata a jiya Asabar a akalla wasu biranen na Libya biyu. Yan tawaye sun gwabza da dakarun da ke goyon bayan Gaddafi a birnin Brega mai arzikin man fetur.
Haka zalika, shaidun gani da ido sun ce an yi kazamin fada a birnin Misrata na yammacin kasar. ‘Yan tawayen na zargin dakarun gwamnati da jefa muggan bama-baman nan masu ‘ya’ya --- zargin da dakarun da ke biyayya ga Gaddafi su ka karyata.
Wani mai magana da yawun 'yan tawayen ya gaya wa kanfanin dillancin labaran Reuters cewa dakarun Mr. Gaddafi sun harba irin wadannan bama-baman a kalla 100 kan yankin da kamfanoni su ke a wannan birnin a jiya Asabar.