Ana Kyautata Zaton 'Yan Boko Haram Ke Kai Hari Jihar Neja

Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau,

Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau,

Akwai alamun hare haren da ake kaiwa jihar Neja 'yan Boko Haram da aka tarwatsa daga dajin Sambisa ne suke haddasasu tare da sace dabbobi da dukiyoyi

Wasu mahara da kawo yanzu ba'a tantance ko su wanene ba dauke da manyan bindigogi sun afkawa wasu kauyuka dake cikin karamar hukumar Rafi.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu sama da mako guda ke nan mutanen na kai hare hare a kauyukan Rafin Sany da kuma Alawa tare da yin awan gaba da tarin dabbobi da duk wata dukiya da suka yi karo da ita.

Baicin sace dukiyoyi suna yiwa mata fyade har da kashe duk wadanda suka yi masu taurin kai.

Malam Namadi Gajere dake zaune a yankin Rafin Sanyi wanda lamarin ya shafa yayi karin haske. Yace an kwashe shanunsa kana an shiga gidansa an yi binciken kwakwaf. Hatta jariri dake kwance kan gado sai da suka saukar dashi suka kwashe shimfidar.

Wani dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar karamar hukumar Rafi Onarebul Danlami Bako yace maharan sun yi kama da 'yan kungiyar Boko Haram. Yace basu da wani imani. Yadda 'yan Boko Haram su keyi haka ma su din su keyi. Ya kira a taimakawa mutanen yankin domin suna cikin wani mawuyacin hali.

Ita ma gwamnatin jihar tace masu aikata ta'asar baki ne da suka shiga jihar kamar yadda kwamishanan labaran jihar Mr. Jonathan Batsa ya fada.

Shugaban karamar hukumar Rafi Onarebul Gambo Tanko yace sun gayyaci sojoji zuwa yankinsu. Su ma 'yansanda sun ce suna iyakar kokarinsu domin kawar da miyagun mutanen.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Btsari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Kyautata Zaton 'Yan Boko Haram Ke Kai Hari Jihar Neja - 3' 06"