Ana kidayar kuri'u a Najeriya

Wani mutum yana kada kuria a zaben majalisar tarayya

Jami’an zabe a Najeriya suna kirga kuri’un zaben majalisar tarayya da aka gudanar jiya

Jami’an zabe a Najeriya suna kirga kuri’un zaben majalisun tarayya da aka gudanar jiya inda aka sami gagarumin fitar jama’a duk da tashe tashen hankali da aka samu a wadansu sassan kasar. An fara kirga kuri’un ne bayan rufe runfunan zabe jiya asabar, domin tabbatar da cewa an yi gaskiya. Jami’an zabe a duk fadin kasar sun rika daga katunan zabe suna kirga kuri’un da karfi gaban masu kada kuri’a da suka taru domin tabbatar da cewa an yi adalci. Jiya da yamma jami’an zabe suka ce wani bom ya tashi a wata cibiyar kirga kuri’u a Maiduguri dake arewa maso gabashin Najeriya. Tun farko, wani bom ya tashi a wata mazaba a birnin ya jikkata mutane da dama. Ranar Jumma’a wani harin bom ya kashe a kalla mutane goma a wani ofishin hukumar zabe dake garin Suleja kusa da Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. Shugaban hukumar zabe Attahiru Jega ya amince da cewa, an sami tashe tashen hankali a wadansu sassan kasar, sai dai bisa ga cewarshi, za a iya cewa, komi ya tafi yadda ya kamata. Ya kiyasta cewa, a kalla kashi saba'in da biyar bisa dari na masu kada kuri’a ne suka kada yi zabe.