Mataimakin gwamnan jihar Filato Mr. Ignacious Longjam ya koka kan yadda jama'ar jihar da dama basu samu katin zabe na din-din-din ba.
Mataimakin gwamnan yana ganin wani mataki ne na hana wasu yin zabe. Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da ya kira inda ya kara da cewa shi bai goyi bayan a daga zaben zuwa wani lokaci ba kamar kiraye-kirayen da wsu suke yi na cewa a dage zaben.
Akan yadda PDP ta fitar da dan takarar kujerar gwamnan jihar Mr. Longjam wanda shi ma ya nemi kujerar yace ba'a yi zabe ba. An dai fada masu, su da yawa cewa basu ci zaben ba. Sun mika kukansu ga uwar jam'iyyar ta kasa amma bata basu amsa ba. Sun rubuta wasikar korafi har sau uku amma shiru kake ji kamar an shuka dusa. Duk da wai an hanashi yace shi bai koma wata jam'iyya ba. Yana nan daram PDP.
Amma hukumar zaben na cewa akwai katuna da mutane basu fito sun karba ba.
Ga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5