Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar INEC Ta Sake Jaddada Cewa Ta Shirya Sosai Don Gudanar Da Zabe


Shugaban Hukumar Zaben Nijeriya (INEC) Furfesa Jega
Shugaban Hukumar Zaben Nijeriya (INEC) Furfesa Jega

A yayin da wasu ke korafin rashin samun katin dindindin na zabe mai kara karatowa, ita ko hukumar zaben Nijeriya (INEC) ta ce kafin lokacin zaben za a warware duk wadannan matsalolin. Don haka ta shirya sosai.

Hukumar Zaben Nijeriya Mai Zaman Kanta (INEC a takaice), ta ce ta shirya soasi don gudanar da babban zabe mai zuwa. Wannan kuwa duk da cewa akwai wasu ‘yan Nijeriya da dama da ba su sami katin jefa kuri’a na dindindin ba.

Shugaban Hukumar Zaben Nijeriya Furfesa Attahiru Jega y ace sun mallaki dukkannin abubuwan da ake bukata don gudanar da zabe mara cikas. ‘Yan siyasa masu yakin nemar zabe sun mai da hankali wajen nemar aibi game da abokan karawarsu. Wannan in ji shi, na barazana ga kwanciyar hankalin da kowannensu ya yi alkawarin jaddadawa.

Wakilinmu a Abuja da ya turo wannan rahoton, Nasiru Adamu Elhekaya, y ace mutane kasa da miliyan 40 daga cikin sama da miliyan 69 da hukumar zaben ta ce ta yi wa rajista ne su ka amshi katin dindindin, alhalin kuwa hukumar Zaben ta jaddada cewa ba za ta amince da amfani da katin wuccin gadi wajen gudanar da zaben ba, kamar yadda Majalisar Wakilai ta fara duban yiwuwar hakan. Nasiru ya ruwaito Daraktan Yada Labarai na hukumar zaben Nick Dazang na cewa, “An tsara zaben ta amfani da katin dindindin, to sai aka sami rashin fahimta tsakanin hukumar da ‘yan Majalisar. Amma mun tuntube sum un masu bayani. Saboda haka a yanzu akwai fahimtar juna tsakaninmu.” Nasiru ya kuma ruwaito Furfesa Jega na kau da duk wata yiwuwar dage zaben.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG