Hukumomi a jamhuriyar Nijar tare da hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kansu, sun kaddamar da shirin wayarda kan jama’ar karkarar Tilaberi, dangane da dalilan kafa dokar ta baci a garuruwan dake fama da matsalar ta’addanci.
Lura da yadda wasu daga cikin mazaunan gundumar Torodi, Say, da Makalondi ke korafi a game da dokar ta bacin da aka kafa masu a karshen shekarar da ta gabata, ya sa hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu soma tuntubar rukunonin al’ummar wannan yanki, da nufin samun hadin kansu don samun nasarar wannan mataki mai nasaba da yakin da jamhuriyar Nijar ta kaddamar.
‘Yan ta’adda a bakin iyakokin Nijar da kasashen Mali, Burkina Faso, sun tada hankalin jama'a, a cewar shugaban kungiyar Transparency International reshen Torodi, Habibou Oumarou.
Bayanai sun yi nuni da cewar an fara samun fahimta a sakamakon irin wadanan taron na musayar ra'ayi a tsakanin mahukunta da talakkawa.
A karshen watan Nuwambar shekarar 2018 ne, gwamnatin Nijar ta bada sanarwar kafa dokar ta baci a gundumomin Say da Torodi dake yankin Tilaberi, bayan la’akari da yawaitar hare haren ta’addancin dake sanadiyar asarar rayukan fararen hula har da jami’an tsaro.
Matakin da wasu mazauna wannan karkara ke guna-guni akansa, saboda a cewarsu barazana ce ga harakokin yau da kullun, ganin irin koma bayan tattalin arzikin da ake kara samu a wasu garuruwa makwafta, biyo bayan kafa dokar ta baci inji su.
Ga rahoton wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka a Yamai, Sule Mumuni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5