Ana Kara Samun Rikici A Siyasar Kasar Haiti

Mazauna kasar Haiti

Kwaramniyar jan kujeru da teburori a cikin zauren majalisar dokokin Haiti ya kawowa zaman majalisar tsaiko a jiya Alhamis da misalain karfe bakwai da rabi na safe.

‘Yan majalisar dattawa guda hudu da wasu mataimakan su, sun ja kujeru da teburori da wasu kaya suka fice da su a cikin zauren majalisar dattawar zuwa waje, minti talatin kafin fara mahawara a majalisar a kan zaben Firai minista mai jiran gado Jean Michel Lapin.

An dakatar da zaman majlisar a jiya Alhamis bayan an kwashe kujeru da teburori a zauren majalisar dattawa. An shirya gudanar da sabon zabe a cikin watan Yuni.

A ranar Laraba ne shugaban majalisar dattawan Carla Murat Cantave ya sanar da aniyarsa ta fara shirya batun zaben, lamarin da ya cije tun ranar 18 ga watan Maris, lokacin da tsohon Firai minista Jean Henry Ceant ya yi murabus, bisa zargin cin hanci da rashawa.

Farko bayyana Lapin a gaban majalisar dattawan a watan da ya gabata, sai da fada ya kaure tsakanin ‘yan majalisar dattawan da suka ciwa juna mutunci har da kaiwa juna naushi, kafin kura ta lafa.