Amurka tana kira kuma zata ci gaba da yin haka kamar yanda sauran kasashen duniya suke yi a kan gudanar da cikakken bincike game da kisan da tsare mutane da kuma bacewar wasu mutanen, inji mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Morgan Ortagus, yana fadawa Muryar Amurka a jiya Alhamis a wani taron maneba labarai.
Ortagus, ya kara da cewa “Muna bukatar wadanda aka riga aka sake su, mutanen da aka kulle su saboda kokarin da suke yi na gani ba a manta cin zarafi da aka yiwa mutane a dandanlin Tiananmen kuma aka ci gaba da tsoratar da masu zanga-zanga da iyalan su.
Shekaru talatin da suka wuce dalibai sun jagorancin wata zanga-zangar neman kafa tsarin demokaradiya a dandalin Tiananmen tare da kuma kin nuna jinin rashin gaskiya da adalci tsakanin shugabanni. Masu zanga-zangar sun kuma yi kira ga sauya yanayin siyasar kasar da kira ga tabbatar da adalci da gaskiya.
Masu raji kare hakkin bil adama sun yi sa ran cewa an kashe dubbannin mutanen da suka yi zanga-zangar yayin da wata motar tanka ta afkawa dandalin Tiananmen.
Facebook Forum