Ana Kara Matsawa Gwamna Ricardo Lamba Ya Sauka Daga Mulki

Masu zanga zanga a Puerto Rico

Dubban masu zanga-zanga sun yi dafifi a babban titin Puerto Rico, su na ta kiran da Gwamna Ricardo Rossello ya yi murabus daga mukaminsa.

Idan aka hada da zanga-zangar ta jiya Litini, an yi kwanaki goma kenan a jere ana ta zanga-zanga a wannan tsibirin kasa, bayan da aka fito da wani kundi mai daruruwan shafuka na irin tabargazar da gwamnan da mukarrabansu su ka tafka a tatattaunawarsu.

Wadanda suka shirya wannan zanga-zangar sun ce ana kyautata zaton miliyoyin mutane za su hallara, wato wajen sulusi guda kenan na yawan mutanen kasar.

An gudanar da zanga-zangar ta jiya litinin din ne bayan da Rossello ya bada sanarwar murabus daga shugabancin jam’iyarsa, tare da cewa ba zai nemi wani wa’adin mulki ba a shekarar 2020; amma bai yi murabus ba.

“Na san na yi kuskure, kuma na nemi ahuwa” a cewar Rossello a wani faifan video da ya wallafa a shafinsa na Facebook.