Washington, D.C. —
Labarun wassaninmu na yau, zai soma ne da kasar Saleo ko Sierra Leone, inda a ke cikin wani abin mamaki da duniya bata taba ganin irin sa ba a wassanin kwallon kafa, bayan da club din Gulf FC da ya wa Koquima Lebanon 91 - 1 yayin da Kahula Rangers ya kafcike Lumbenbu United da ci 95-0 a rukuni na 2 na wassanin kwallon kafa na kasar Saleo ko Sierra Leone.
Tuni dai, hukumar kwallon kafa ta kasar Saleo ko Sierra Leone, ta ce, ta shiga bincike mai zurfi a kan wadannan wassanin, kasancewar a karawar kungiyoyin akwai inda dan wasa guda ya ci kwallaye 30 shi ka daya, yayin da akwai inda alkalin wasa ya yi murabus a lokacin rabin hutun wasa da korar '
'yan wasa babu gaira babu dalili ta hanyar basu jan kwali.
Hukumar kwallon kafa ta Saleo ko Sierra Leone, ta fitar da sanarwa a ranar Litinin da ta gabata ta cewa, wadannan kungiyoyin da ke nema hawa rukuni na farko na kwallon kafa na kasar, sun jefa ta cikin shakkun akwai coge a lokacin wadannan wasannin kuma za ta aiwatar da bincike mai zurfi a kai.
------------------------------------------------------------------------------------------
A cigaba da wasannin kwallon kafa na kofin mata na nahiyar Turai da ke wakana yanzu haka a kasar Ingila, a jiya Litinin, 3 Layone na matan na Ingila sun wa takwarorinsu na Norwey ko Norvege cin kaca 8 - 0.
Abin ya zo wa masu sha'awar wasannin kwallon kafa na mata mamaki, saboda daga cikin 'yan wasan na Norwey ko Norvege akwai Ada Hegerberg shahararrar 'yar wasar kwallon kafar kasar da ta zama ta farko a tarihin kwallon kafa ta duniya da ta taba lashe ballon d'or na France Football a 2018, da ke bugawa club din Olympique de Lyon na kasar Faransa.
A jiya, Ireland ta Arewa, ta sha kashi 0 - 2 a hannun Austria, yayin da a shekaran jiya Faransa ta kakabike Italiya da ci 5 -1.
A yau an kara tsakanin Finland da Denmark, yayin da a ka kece reni tsakanin Spain da Jamus.
-----------------------------------------------------------------------------------------
A gasar tseren keke mafi farin jini a duniya na Tour de France, a yau ana rana ta 11, bayan hutun da yan wasan suka yi a ranar jiya da ma binciken cutar korona - bairis da masu shirya wasan suka yiwa kowace tawaga da ke cikin wannan gasar ta bana, inda ba'a samu ko mutun guda ba dake dauke da wannan cutar ta mashako.
Har yanzu dai, Tadej Pogačar dan kasar Sloveniya ne ke kan gaba yayin da Geraint Thomas dan kasar Wales ko Payas Des Galles ke na 2 sai David Gaudu dan kasar Faransa a matsayin na 3.
A yau dai, tseren na bana na kwanaki na 11, inda 'yan tseren suka tasahi daga Haute-Savoie Zuwa les Alpes.
A ranar 14 ga watan Yuli ne za a kammala wannan gasar ta tseren keke ta kasar Faransa na Tour de France dake karon ta na 109 a bana a Fadar Gwamnatin kasar da ake kira Champs Elysées.
Saurari rahoton Harouna Bako:
Your browser doesn’t support HTML5