Wani likita Dr. Dalhatu, yace ana iya kamuwa da cutar Ebola ta hanyoyi da dama kamar saduwa da mai dauke da cutar, karin jinni ko kuma duk wani nauin ruwa ko gumi.
Dr. Dalhatu ya wannan bayani ne a wata hira da suka yi da wakilin mu Baba Yakubu Makeri a Ghana, inda ake gudanar da taro akan cutar Ebola wace hukumar kiwon Lafiya ta Duniya, ke daukar nauyin gudanarwa a Accra, babban birnin kasar Ghana.
Cutar Ebola ta kashe mutane fiye da dari hudu da hamsi a kasashen Liberiya, Guinea da kuma Sierra Leone.
Wannan sabon adadin, ya nuna karuwar kashi 38 cikin 100 na wadanda cutar ta kashe daga adadin da aka bayar a makon da ya shige.
Kasashen Afirka su 11 ne suka tura wakilansu zuwa wurin taron, ciki har da na Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5