Ana Jiran Matakin da Shugaba Buhari Zai Dauka Akan Maina

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da ake jira ya dauki mataki akan Maina da ma wasu

Tuni shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya ta mikawa shugaban kasa rahoto akan dawo da Abdulrasheed Maina kamar yadda ya bukata, yanzu shi ake jira ya bayyana matakin da ya dauka akan dambarwar

Shugabar ma’aikatan Najeriya Winifred Ita Oyo ta mikawa shugaban kasa rahoton da ya nema kan dambarwar da ta biyo bayan batun dawo da tsohon shugaban kwamitin fansho Abdulrasheed Maina bakin aiki tare da kara masa girma.

Abdulrasheed Maina wanda aka kora daga aiki

Ta mika rahoton ne ta hannun Abba Kyari shugaban ma’aikatan fadar gwamnati.

Jiya da aka yi taron Majalisar Zartaswa na mako-mako, duk wadanda aka ambaci sunayensu cikin dambarwar irin su ministan shari’a Abubakar Malami sun halarci taron sai dai Janar Abdulrahaman Dambazau da aka ce ya yi balaguro zuwa Saudiyya.

Kawo yanzu babu wani mataki da shugaban kasa ya dauka, ke nan watakila yana nazari akan rahoton kamar rahoton sakataren gwamnati Babacir Lawal da aka mikawa shugaban tun da dadewa.

‘Yan Najeriya dai sun sa ido tare da kunnuwansu a kasa komene zai faru.

Amma Dr Garba Abari na Hukumar Wayar Da Kawunan Jama’a ya ce ba za’a rufe asirin duk wanda aka samu da laifi ba. Ya ce akan batun yaki da cin hanci da rashawa gwamnatin Buhari bata da shafaffu da mai.

Baicin wannan batun har yanzu ma fadar shugaban kasa bata ce komi ba akan shugaban Hukumar Inshorar Kiwon Lafiya Farfesa Yusuf Usman wanda Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta kasa ta dakatar tsawon wattani uku.

Bayan karewar wa'adi’n, ministan kiwon lafiya Dr Isaac Adewole ya tsaiwata dakatarwar da yanzu ta zaman har illamasha-Allahu.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Jiran Matakin da Shugaba Buhari Zai Dauka Akan Maina - 2' 07"