Shi dai shugaba Buhari, a wani sakon da aka wallafa a shafin Shugaban kasar na Twitter, ya bada umurnin a kori Abdulrasheed Maina daga aiki nan take, a kuma yi bincike game da yadda aka yi ya koma aikin gwamnati.
Har-ila yau shugaba Buhari ya umarci shugabar ma'aikatan gwamantin tarayya, Oyo-Ita Winifred Ekanem, da ta mika rahoton binciken ga ofishin shugaban ma'aikata na fadar shugaban kasa, Abba Kyari akan lamarin.
To sai dai masana harkar sharia a kasar irinsu Barrister Sunday Joshua Wigra, wani lauya mai zaman kansa a kasar, na ganin akwai gyara a wannan kora ta Mainan.
Ibrahim Abdul’Aziz na da karin bayani
Facebook Forum