Wannan ya hada da hadin gwiwar takwarorinsu na Rasha, lamarin da ya ta da hankalin jama’ar iyakokin kasashen biyu.
Labarin wanda ya karade kafafen sada zumunta na cewa ‘yan ta’addar da ke da sansanin a arewacin Mali cikinsu har da mayan kwamandoji irinsu Iyad Agali da Amadou Kounfa sun arce zuwa wajejen gundumar Ayoroun jihar Tilabery sakamakon barin wutar da suka sha daga wani hadin gwiwar sojan FAMA na Mali da takwarorinsu na kasar Russia.
Wannan al’amari ya ta da hankalin jama’a a garuruwan da ke iyakar Nijar da Mali kamar yadda wani mazaunin Ayorou ya shaidawa Muryar Amurka ta wayar talaho.
Kawo yanzu hukumomin Nijar ba su tabbatar da faruwar wannan al’amari ba, haka kuma ba su karyatar da shi ba.
Jami’in kare hakkin dan adam na kungiyar ROADDH Son Allah Dambaji, na mai kiran mahukuntan su fito su yiwa ‘yan kasa bayani don kada masu yada jita-jita su haddasa rudani a tsakanin al’uma.
Manyan kasashen da suka ci gaba kan amfani da fannin sadarwa wani zubin a matsayin makamin yaki don tsorartar da abokin gaba kamar yadda irin haka ke wakana a yanzu haka a yankin sahel inji mai sharhi akan sha’anin tsaro Abdourahamane Alkassoum.
Amma wata majiya mai tushe ta bayyana cewa farmakin da sojIn Barkhane na Faransa suka kaddamar a kwanakin nan da hadin gwiwar rundunar mayaka ta Operatin Takoba ne ke firgitar da ‘yan bindigar arewacin Mali suka fantsama zuwa neman mafaka.
Amma kuma har Izuwa yau ba wasu bayanai da ke tabbatar da cewa sun tsallako Nijar.
Kuma majiyar ta kara da cewa kawo yanzu dakarun Rasha 400 kacal ne ke Mali wadanda ke aikin ba da horo ga dakarun FAMA abin da ke nunin babu kamshin gaskiya a farmakin da ake cewa sun kaddamar a wannan mako.