Babban jami’in aikace-aikacen hukumar ta UNDP a Najeriya, Majo Janar Salihu Uba Mai ritaya, yace taron nada muradun yada sabon daftarin wanzar da zaman lafiya da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu a bara.
Uba yace UNDP ta fara wannan shiri ne a wannan shekara domin tallafawa gwamnati wurin watsa kasidu da shugaban kasa ya sanyawa hannu saboda mutane su gane abin da yakamata su yi idan sun ga abu na faruwa kana su san yanda zasu yi hulda da juna cikin aminci ba tare da tashin hankali ba.
A cikin watan Agunstan shekarar 2017 ne shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan wani daftari da zai wayar da al’umma a kan abubuwa da yakamata su yi a matsayinsu na ‘yan kasa musamman kyautata zamantakewa tsakanin al’umma. Haka Zalika daftarin yana wayar da gwamnati da kungiyoyin jama’a da sauran masu ruwa da tsaki a kan zaman lafiyar kasa.
Babban jami’in aikace-aikacen hukumar ta UNDP, Majo Janar Salihu Uba Mai ritaya, ya yi kira ga mutane sun nemi sanin abin da daftarin ya kunsa domin su taimakawa gwamnati, da yanda zasu taimakawa hukumomin tsaro da ma yanda zasu taimakawa junansu.
Ga dai hirar wakilinmu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari da Majo Janar Salihu Uba Mai ritaya:
Your browser doesn’t support HTML5