Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro da Juan Guaido, babban mai kalubalantarsa a siyasance, wanda ya kuma ayyana kansa a matsayin Shugaban kasa na wuccin gadi, kowannensu ya na shirin gudanar da gangamin ranar Ma’aikata, kishiyoyin juna a yau dinnan Laraba, a cigaba da fafatawar da su ke yi na mulkin kasar, wadda tattalin arzikinta ya durkushe.
Bangarorin biyu na shirin gudanar da gangamin ne bayan mummunan zangar-zangar da aka yi kan titunan Caracas, babban birnin kasar, bayan da Guaido mai samun goyon bayan Amurka ya yi kira ga sojoji da su yi watsi da shugabancin Maduro, su canza sheka zuwa bangarensa a wata fafatukar da ya kira, “Fafatukar Neman ‘Yanci.” Guaido ya tsaya kusa da dan’adawa Leopoldo Lopez, wanda Maduro ya masa daurin talala, amma sojojin da ke goyon bayan Guaido su ka sako shi, kamar yadda ya bayyana.
Lopez ya saka wani hoton wasu mutane cikin kakin soji a kafar twitter, tare da sako mai cewa, “Venezuela: a mataki na kawo karshen babakere, an shiga gwagwarmayar neman ‘yanci.”