Karuwar jami’iyyu masu ra’ayin mazan jiya da masu sassauci ra’ayi bai yi wani tasiri ba har sai da aka kafa babbar jami’iyar adawa ta Popular Party.
'Yan gurguzu sun lashe zabe. Kyakkyawar makoma ta yi nasara a kan abin da ya shude, inji Firai minister Predro Sanchez yana fadawa manema labarai a waje helkwatan jami’iyarsa a Madrid. Yace akwai yiwuwar kafa gwamnatin hadaka tare da jami’yyun ‘yan mazan jiya da masu sassaucin ra’ayi manyan abokan hamayyarsa.
Bayan kirga kashi 99 cikin dari na kuru’un da aka kada, jami’iyar yan gurguzu mai mulki ta lashe kashi 28 cikin dari ta kuma samu kujeru 123 a cikin kujeru 350 a majalisar dokoki adadin da ya haura kujerunta a baya da kujeru 40. Amma ita jami’iyar Popular party ta ‘yan adawa ta samu kasa da kashi 17 cikin dari kana ta rashi kujerunta da dama inda ta sauko daga kujeru 120 zuwa kujeru 65.
Sakamakon dake fitowa ya gurgunta aniyar kafa hadaka da shugabannin jami’iyyun masu ra’ayin ‘yan mazan jiya suka tattauna tsakaninsu da suka hada da PP da Ciudadanos da kuma Vox
Facebook Forum