A yau Laraba ake ganin Majalisar Dokokin Amurka za ta kada kuri’ar tsige Shugaba Donald Trump, wanda zai zama Shugaba na uku da ya taba fuskantar tsigewa a tarihin kasar.
Kamar yadda Majalisar ta gindaya wasu ka’idoji da za a bi, a wani zama da ta yi a jiya Talata, za a kwashe tsawon sa’o’i 6 ana muhawara akan hujojin da aka gabatar, da suka hada da cewa shugaban ya yi amfani da karfin mulki ba bisa ka’ida ba.
Ya bukaci kasar Ukraine da ta shiga cikin harkokin zaben Amurka mai zuwa wato na shekarar 2020, kana da hana Majalisa ta yi aikinta, wanda ya hana hadimansa su amsa sammacin gayyata da majalisar ta aika masu, don su zo su ba da ba'asi, kana da wasu takardu da suka shafi binciken.
Za a fara kada kuri’ar ne da yammacin yau, wanda a dai-dai lokacin kuwa shi ma Shugaba Trump zai gabatar da jawabi a wani taron yakin neman zabensa a jihar Michigan.
‘Yan jam’iyyar Demokrat ne dai ke da rinjaye a majalisar, wanda hakan ke nuna cewar kudurin na tsige Shugaban zai sami amincewa ko da kuwa ‘yan adawa na jim’iyyar Republican ba su amince ba.
Majalisar Dattawa kuma za ta dubi lamarin a watan Janairu, inda ganin cewar ‘yan Republican ke da rinjaye a Majalisar ta Dattawan, babu alamun za ta amince da batun tsige shugaba Trump.