Ko da ya ke gwanatin Najeriya ta riga ta dora alhakin mutuwar wadannan mutane akan masu wannan haramtacciyar matatar mai, galibi, musamman masu fashin baki, na cewa sakaci da kuma gazawar gwamnati wajen samar wa al'umma abin yi ne ya sa ake tururuwa zuwa haramtattun matatun mai.
Haka kuma jama'a da dama na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu akan wannan ibtila'in da ya fada wa al'ummar jihar.
Wani marubuci Dakta Amanze Obi ya bayyana cewa, "Abin takaici ne satar mai na faruwa a gaban hukumomin tilasta doka kuma basa komai game da ita, saboda duk an bata su. Kuma zaka tarar cewa galibi masu satar mai matasa ne da basu da aiki, kuma gwamnati bata tallafa musu, da yasa suke neman hanyar taimaka wa kansu. Abin da suke yi bai dace ba, amma halin da suka tsinci kansu ne yasa suke yi abin da bai dace ba, kuma hukumomi basa daukar mataki saboda suna daya daga cikin matsalolin da ke addabar kasar."
"Gazawar gwamnati wajen samar wa jama'a aiki ne ya janyo wannan. Kuma gazawar gwamnati wajen farfado da matatun man mu ya samar wa wasu haramtattun wuraren gudanar da harkokinsu," inji Dakta Osita Nwosu.
A nasa bayanin da Mista Maurice Ogbonna, wani dan asalin karamar hukumar Ohaji/Egbema, inda gobarar ta auku, ya bayyana cewa, "Gwamnati ta ki ta kula da su tun da dadewa. Shi ya sa matasan yankin ke fita suna neman hanyoyin raya kansu."
"Hanya kadai da za a iya daina irin wannan ta'adin ita ce gwamnati dauki matakai kwakkwara don tabbatar da cewa an samar wa akasarin matasanmu da ke kara zube abin yi, saboda idan suna da abin yi ba za su tsunduma cikin satar mai ba. Kuma idan muna da jami'an tilasta doka wadanda zasu tabbatar cewa ba'a jure wa irin wannan haramtaccen aiki ba, tabbas mutane zasu daina," inji Dakta Amanze Obi.
Yanzu rundunar 'yan sandan jihar Imo ta ce tana gudanar da bincike kan wannan gobarar, da zummar gano ainihin musabbabinta, yayin da gwamnatin Najeriya ta bada umurnin kama masu wannan haramtacciyar matatar mai.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5