Masu aikin ceto a Thailand suna aiki cikin gaggawa su ceto kungiyar yan wasan kwallon matasa da suka makale a cikin wani kogon da ambaliya ruwa ya tabakawa sama da mako guda, kafin ruwan sama kamar da bakin kwarya da za a samu a cikin yan kwanaki masu zuwa kamar yanda hasashe ya nuna.
An gano matasan 12, yan shekaru 11 zuwa 16 da mai horar da su dan shekaru 25 a ranar Litini hade wuri guda a kan wani dutse a can cikin kogunan Tham Luang.
A halin da ake ciki kuma, hukumomi suna kokarin jan ruwa daga cikin kogon, amma ganin za a samu ruwan sama mai yawa kamar yanda hasashe ya nuna, yaran zasu bukaci amfani da rigar da zata hana su nitsewa cikin ruwa, yayin da kwararrun zasu rika basu shawara abinda zasu yi, inji ministan harkokin cikin gida Anupong Paojinda.
An ce yaran da mai horar dasu suna cikin kasala. Sojojin kundubala na mayakan ruwan Thailand guda bakwai da suka hada da ma’aikatan lafiya ne suke kula da yara kuma suna tare da su a cikin kogon.