Ana Fuskantar Karuwar Cin Hanci Da Rashawa A Nijer

HALCIA - Nijar

A yayin da kasashen duniya ke bukin tunawa da ranar yaki ta cin hanci a yau 9 ga watan Disamba, shugaban hukumar yaki da cin hanci a jamhuriyar Nijer, Mai shara’a Mai Moussa Alhaji Basshir ya bayyana cewa matsalar cin hanci na kara tsananta a ma’aikatun gwamnati.

Sai dai yace shi da mataimakansa za su kara jan damara domin tunkarar wannan babban kalubale.

Cin hanci da rashawa wata matsala ce da ta shafi kusan kowane fanni a nan Nijer to amma kuma abin ya fi kamari a wajen jami’an tsaro kamar yadda bayanan kurar jin ra’ayin jama’a suka nuna, inji shugaban hukumar yaki da cin hanci HALCIA, mai shara’a Mai Moussa Elhadji Basshir.

Rashin hukunta masu aikata cin hanci da jahalcin jama’a a game da koma bayan da wannan al’amari ke haddasa wa kasa na daga cikin manyan dalilan da ke janyo karuwar cin hanci a Nijer. Shugaban HALCIA yace ya na da kwarin guiwa al’amura zasu canza.

Kungiyar yaki da cin hanci ta Transparency International ta bayyana Nijer a matsayin kasa ta 8 mafi cin hanci a Afrika ta yamma a shekarar 2021.