Dr Haliru Alhassan karamin ministan kiwon lafiya a Najeriya ya bayyana ire-iren nasarorin da suka samu wurin dakile cutar ebola.
Yace sun samu nasara gagaruma wajen tsayar da cutar inda ta fito a Legas da kuma rashin bazuwa koina cikin kasar. Kamar yadda aka sani cutar ta shigo ne ta hanyar bakon amana da ya shigo amma ya ci amanar kasar domin yasan yana dauke da cutar. Kafin bullar cutar kasar bata da wani shirin yadda za'a tunkareta.
Nasarar da suka samu a Legas da Enugu zata taimakesu su yi yaki da Fatakwal domin su hanata yaduwa. Ministan ya kara da cewa akwai wasu matakai da suke dauka domin gano wadanda suke dauke da cutar.
Akwai hanyoyin da suke bi wadanda ba zai so ya bayyana ba amma suna nan suna dubawa kuma duk wanda yake dauke da cutar zasu wareshi. Ko yana gidansa ko ya je wani wuri duk zasu gane. Sun daki matakan da zasu tabbatar cewa irin abun da ya faru bai sake faruwa ba.
Kawo yanzu ma'aikatar kiwon lafiyar kasar tana samun tallafi akan cutar ebola daga kasashen ketare. Kungiyar lafiya ta duniya da kungyar bincike ta Amurka da makamantansu duk sun kawo taimako da manya-manyan masana wadanda sun yi aiki da masu dauke da cutar sun kuma warkar dasu.
Akwai maganin da aka samu amma na gwaji ne ba'a kai lokacin da aka gwadasu ga mutane ba. Sun yi anfani da kwararru su bada maganin ta yadda ba zai yiwa mutane illa ba.
Kimanin ma'aikatan kiwon lafiya ashirin ne cutar ta kashe a kasar Saliyo inda ma ma'aikatan kiwon lafiyan suka shiga yajin aiki domin rashin biyansu alawus nasu. Ita kuwa kasar Liberia ta dage takunkumin killacewa da ta sanyawa wata anuguwa ta karamin karfi a kokarin hana yaduwar cutar.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.
Your browser doesn’t support HTML5