A safiyar yau Alhamis ne hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya - NCDC, ta fitar da adadin da ke nuni da cewa an sami mutane 535 dauke da cutar a jiya Laraba.
Hukumar ta NCDC ta bayyana wannan adadi na mutane 535 da suka kamu da cutar da cewa ya zarce adadin mutane 404 da aka samu na ranar 27 ga watan Yuli, adadin da hukumar ta rawaito cewa shi ne mafi yawa a aka samu rana daya a cikin watanni hudu a kasar.
Kazalika hukumar lafiya a matakin farko ta bayyana cewa Jihar Legas ce ke kan gaba cikin jihohin da ke da yawan wadanda suka kamu da cutar.
Hukumar ta kuma bayyana alhininta akan rasa mutane biyar sakamokon cutar a Jiya Laraba.
Wannan kuma ya sa jumlar adadin wadanda aka rasa ya kai 2,139 a kasar baki daya.