A yayinda ake dab da rufe hada hadar zawarcin ‘yan wasan kwallon kafa na shekara 2017. Yanzu haka kungiyoyi da dama musamman na nahiyar turai sun dukufa wajan ganin sun kammala saye da sayarwa da kuma bada aron ‘yan wasan kwallon kafa kafin a rufe cinikaiyar a ranar Alhamis 31/8/2017.
Kungiyar kwallon kafa ta Paris st Germain, da Monaco, sun cimma yarjejeniya kan matashin dan wasannan Kylian Mbappe, a matsayin aro, kungiyar ta Monaco, ta amince da haka da alkawarin PSG zata sayi dan wasan nan gaba, akan kudi fam miliyan £166.
Liverpool, ta tsaida ranar litinin da cewar ita ce rana ta karshe da ta ba kungiyar Barcelona, ta kammala cinikn dan wasan tsakiyar Philippe Coutinho, a kan kudin da ta bukata ko kuma a hakura.
Arsenal tana shirin sayen dan wasan Real Madrid, Marco Asensio, a kan kudi fam miliyan £75 kafin a rufe cinikaiya.
Akwai yuwar kungiyar Arsenal, zata rasa’ yan wasanta da dama kamar su kieran Gibbs, Alex Oxlade Chamberlian, Lucas Perez, da kuma dan wasan bayanta Shkodram Mustafi, kafin a rufe hada hadar ‘yan wasa.
Chelsea tace zata biya fam miliyan £30 wajan sayen dan wasan Leicester city Danny Drinkwater, Stoke city ta amince da cinikin fam miliyan £15 tsakaninta da Tottenham kan sayen Keven Wimmer.
Everton ta ce zata biya fam miliyan £40 a kan sayen dan wasan gaba na Leicester city, Jamie Vardy, Westham zata sayar da dan wasan Sporting Lisbon, William Carvalho, a kan kudi fam miliyan £38 inda zai zamo dan wasa mafi tsada a kungiyar.
Your browser doesn’t support HTML5