Yanzu haka ana dab da hana masu shiga da dabbobi Jihar Legas shiga da su, muddin ba’a cimma matsaya ba tsakanin gwamnatin Legas, da fataken dabbobin dangane da Karin kudin haraji.
A halin da ake ciki, an ja layi tsakanin gwamnati, da fataken dabbobin gab da bukukuwan babbar Sallah wadda ake yanka dabbobi.
Fataken dabbobi a halin yanzu sunce baza ta yiwu ba a kara musu haraji. Fataken sun bayyana cewa Sakataren harkokin Noma da Gandun Daji na Jihar, Mr. Yakubu Bashorun, shine ya bada sanarwar karin haraji akan inda ake ajje motocin dabbobi a kasuwarsu, da kuma biyan wani haraji ga wanda gwamnati ta nada ya kula da kasuwar ta shanu.
Shugaban Miyatti Allah na Jihar Legas, Alhaji Abdullahi Laliga cewa yayi “ba gaskiya bane a ce, shi mai katuwar mota, ya karbi kudi ba, ko ya bayar”.
Sashen Hausa na Muryar Amurka yayi kokarin tuntubar Mr. Yakubu Bashorun amma bai mayar da martani ba.
Your browser doesn’t support HTML5