Amy Coney Barrett wadda Shugaba Donald Trump ya zaba don zama mai shari’a a kotun kolin Amurka zata ta Majalisar Dattawan kasar yau Laraba don ci gaba da amsa tambayoyi bayan wani zama na kusan sa’o’i 12 da aka yi da ita jiya Talata inda ta ki ta amsa wasu tambayoyi daga Sanatoci game da yadda zata yanke hukunci akan shari’a da zata fuskanta idan aka tabbatar da ita don cike gurbin da ke babbar kotun kasar.
Barret ta fada wa Kwamitin Shari’a ta Majalisar Dattawan da ke zaman amincewa da ita cewa ra’ayinta da addininta ba zasu taka rawa wajen yadda zata yanke hukunci a shari’a ba.
Barrett, a tambayoiyin da yan Republican 2 suka yi mata da farko, wato shugabar kwamitin sanata Lindsey Graham, da Sanata Chuck Grassley, da kuma yan Democrat 2 Sanata Dianne Feinstain da Patrick Leahy, ta ki ta fadi yadda zata yanke hukunci akan dokar kotu ta shekarar 1973 game da damar zubar da ciki a Amurka, da ‘yancin mallakar bindiga da kundin tsarin mulki ya tanadar, kuma a zaman shari’ar da za a yi wata mai zuwa akan tsarin kiwon lafiya tana gani ya kamata dokar ta kasance yadda ta ke ko a’a.