Ana Ci Gaba Da Tashin Hankali A Arewa Maso Gabashin Brazil

Yanzu haka ana ta kone-kone a jihar Ceara dake arewa maso gabashin Brazil, an fara tashin hankalin ne kwana daya bayan da aka rantsar da sabon shugaban kasar Jair Bolsonaro.

Hare-haren bama-bamai ya mamaye jihar Ceara dake arewa maso gabashin Brazil, inda ya ci gaba a jiya Lahadi duk da jibge rundunar ‘yan sanda masu horon soja da yawansu ya kai a kalla 300, domin taimakawa gurin kwantar da tarzoma.

Ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar ta ce an kona bus-bus da kananan motoci kana, an kaiwa gidajen mai hari a Fortaleza da babban birnin kasar da ma wasu birane shida a cikin kasar. ‘Yan sandan sun kashe mutane biyu a cikin wata musayar wuta. Sama da mutane 100 ne ake tsare dasu tun lokacin da rikicin ya barke a ranar Laraba.

Jibge rundunar tsaro a Ceara na zuwa ne wuni guda bayan da aka rantsar da sabon shugaban kasar Jair Bolsonaro, na jam’iyar masu ra’ayin mazan jiya kuma tsohon kaftin soja, wanda aka zabe shi a kan manufarsa na sa kafar wando daya da miyagu da kuma sakarwa rundunar tsaro mara su yi aiki a kan miyagun.

Tun da farko ya yabawa mataki da rundunar tsaron ta dauka, yana mai cewa mutanen Ceara na bukatar taimako a wannan lokaci.