‘Yan sandan Burtaniya sun tsare wasu mutane uku sakamakon binciken da ke da alaka da harin Bom din da aka kai ranar Litinin din da ta gabata, a lokacin wani wasan raye-raye da kade-kade a Manchester.
A jawabin da Ofishin ‘yan sandan Greater Manchester suka bayar a yau Laraba, cewa anyi kamen ne bayan jami’an sun sami izini a Kudancin Manchester. Babu wani bayani akan kama mutane ukun ko kuma na hudun da aka kama jiya Talata, wanda aka bayyana a matsayin dan shekaru 23, su ke da hannu a harin.
Ministar harkokin cikin gidan Birtaniya Amber Rudd ta fada a yau Laraba cewa Jami’an tsaron Burtaniya sun san da dan kunar bakin waken, wanda aka bayyana sunan sa da Salman Abedi dan shekaru 22, kafin Kai harin.
Haka kuma ta fadawa Kafar yada labarai ta BBC cewa “Akwai alamun ba shi kadai yake aiki ba”
Masu bincike na ta fadada bincikensu tun ranar Litinin don gano ko harin bam din na cikin wani babban shiri na wata kungiya.
Shugaban yaki da ta’addanci na bangaren ‘yan sanda Mark Rowley, ya ce an samu cigaba a binciken a jiya Talata ta hanyar samun alamu da yawa. Amma yace har yanzu Jami’ai baza su iya cewa Abedi shi kadai ya aiwatar da harin ba.
Bayanin nasa ya zo daida lokacin da aka kara kafa matakan tsaro a kasar don kare aiyukan ta’addanci, sakamakon alamu na yiwuwar kai wani harin wanda bai da makawa.