Mr. Laurent Gbagbo, wanda abokin takararsa Alassane Outtara, ya kada a zaben shugaban kasa, ya kuma ki amincewa da kayen da aka yi masa, yanzu an kama shi yana tsare. Babban jami’in dake baiwa Laurent Gbagbo shawara a Faransa, Toussaint Alain, a tattaunawar da gidan rediyon Amurka VOA yayi dashi yace rundunar sojin Faransa ta musamman ce ta kama Gbagbo da ransa a gidansa dake birnin Abidjan yau litinin.Kamfanin dillancin Labaran Faransa ya jiwo daga wajen Jakadan Faransa a Ivory Coast yana tabbatar da kamun da aka yiwa Laurent Gbagbo.
Tun farko shaidun gani da ido sun ce sunga motocin yakin Faransa na dannawa a guje zuwa gidan da Laurent Gbagbo ya killace kansa a ginin karkashin kasa, sannan sojin dake biyayya gareshi suna gadinsa.
A makon jiya ne sojin dake biyayya ga Alassane Ouattara, wanda kasa da kasa suka amince da shine ya sami nasara a zaben shugaban kasar Ivory Coast suka kaiwa gidan Gbagbon hari sannan suka yiwa gidan da’ira, amma basu sami nasarar tilasta masa ya mika kai ba.
Laurent Gbagbo, yaki sauka daga kujerar mulkin Ivory Coast bayan bayyana sakamakon zaben da aka kada shi, MDD ta kuma amince da sahihancin sakamakon zaben na watan Nuwamban da ya gabata.Anji mazauna birnin Abidjan na cewa tun da hantsi mayakan Alassane Ouattara suka gwabza fada da sojin dake yiwa Laurent Gbagbo biyayya kafin isar sojin Faransa da suka sami nasarar kama Laurent Gbagbo.Har yanzu dai mayakan dake biyayya ga Alassan Ouattara sun dauke Gbagbo dagagidansa suka maida shi “Golf Hotel” inda ake ci gaba da tsareshi, sai dai ya zuwa yanzu ba’a kama manyan mukarraban Gbagbo dake bashi shawara da jan ragamar mulkin Ivory Coast, jami’ai irin su “Simone Gbagbo da M. Ble”.