Ana ci Gaba Da Tantance Wadanda Suka Mutu a Saudiyya

  • Ladan Ayawa
Har yanzu ana ci gaba da tantance adadin mutanen da suka mutu na kasashe daban-daban wadanda turmutsin nan ya rutsa dasu a kasar Saudiyya.

Musammam wadanda basu da basu fito ba kuma ansan suna da yawan gaske sune yan Najeriya sune wadan da a kalla ana ta bada labarin ba aga wani ba, ana jin wane ya rasu inda harma ake fadan cewa ya shafi wasu sarakunan gargajiya masu martaba na biyu daga Najeriya din.

Sunayen ne dai ba a fito dasu a hukumance an bayyana ba, amma tabbas lokacin da aka fito da wannan sakamako, kamar yadda wakilin Muryar Amurka dake kasar ta Saudiyya Nasir Adamu El-Hikaya ke cewa YAWAN Yan Najeriya da suka rasu zasu kai na 3 mafi yawan mutane da suka rasu bayan kasar Iran da kasar Morocco.

Nasir yace adadin yan Najeriya ya haura 35 a bisa bayanan dake fitowa.

Yace har yanzu akwai mutane wajen jifar shaidan, domin kamar kasha 25 suka bar tantunan a yau asabar, kamar yadda aka saba mutum kan iya kwanaki biyu ko ukku a wannan wuri.

Shugaban tawagar addinin Musulunci na Najeriya Mai martaba sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi yace kwanaki ukku zaiyi a wadannan tantuna, don haka yana baiwa mutane shawarar suyi kwanaki ukku, dama dai yan Najeriya basu faye yin kwanaki ukku ba.

Amma mutanen sauran kasashen Larabawa da Asiya da mutanen Indonesia, da Malasiya yawanci sukan zauna su cika wadannan kwanakin.

Halima Djimrao ta tattauna da Nasir Adamu El-Hikaya da kuma Mustapha Kady shugaban Hadakar kungiyar kare hakkin bil adama dake kasar Niger wadda ake kira (CODDEU) a takaice.

Ga Halima da ci gaban hirar.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana ci Gaba Da Tantance Wadanda Suka Mutu a Saudiyya '7 09''