Al'ummar Kristoci na Damagaran a Nijar na shirye shiryen bikin Kirisimeti kamar yadda wanin Limamin Majami'ar Darikar 'Evangelical' Yahaya Arzuka bayyana, tare da cewa suna shirye shiryen yin wakoki da wa'azin da za a gabatar ranar bikin na Kirisimeti.
Ya kara da cewa, za su mayar da hankali akan dawowar Yesu Al-Masihu duniya tare da nunawa mutane cewa babbu wani hanyar ceto sai ta hannunsa. Muhimmin abin da za su jadadda a zagawoyar Kirisimetin shine zaman lafiya.
Inda Malam Yayaha yace, suna cikin addu'a a kullum akan zaman lafiya domin idan babu zaman lafiya komai barkicewa yake. Ya kara da cewa zasu jaddadawa mabiyansu maganar bautawa Allah da zuciya daya kuma a kawar da mugunta a koma ga Allah.
Malam Arzuka ya bayyana cewa saka sababbin kaya ba shine muhimmin abu a bikin na addini ba, face abin da yake zuciyar mutum shi ya fi muhimmanci.
Daga karshe Malamin ya yabawa yanayin zaman lafiya da suke yi da 'yan uwansu Musulmin Nijar, ya kuma basu tabbacin ba za su manta da su ba a dukkan lamuransu, domin a cewarsa duk zamansa a cikin Musulmi ba su taba nuna mishi tsangwama ba.
Ga cikakken rahoton wakiliyarmu daga Nijar.
Your browser doesn’t support HTML5