Ana Ci Gaba Da Sa In Sa Kan 'Yar Tinke A Jam'iyyar APC

Jigo a siyasar jihar Buachi a yankin arewa maso gabashin kasar Najeriya Alhaji Hassan Sharif Sarkin arewan Bauchi, ya ce sam ba amfanin yin zaben fidda gwani na APC ta hanyar ‘yar tinke don hakan a ra’ayin sa zai kawo rudu ne kawai da ma haddasa magudi.

Hassan Sharif da ke zantawa da kafafen labarun ketare a Abuja, ya ce hatta zabar hanyar ‘yan tinke ga fidda shugaba Buhari a takarar shugaban kasa ba daidai ba ne duk da ma shugaban ya kama hanyar nasarar zaben ba hamaiya.

Kazalika Hassan Sharif ya yi watsi da rade-radin da ke cewa gwamnan Jahar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ba shi da goyon bayan jama’a biyo bayn yadda wasu su ka yi murabus daga gwamnatin sa ciki har da mataimakin Nuhu Gidado.

Amma daya daga cikin manyan ‘yan siyasa da ke batun ingancin zaben ‘yar tinke Dr.Muhammad Ali Pate ya ce tsarin shine kawai mafita ga APC.

Ali Pate ya ba da labarin tura wakilin sa taro a matakin jiha don daidaitawa kan zaben fidda gwani amma wakilin ya fuskanci turjiya.

Za a jira a ga yadda wannan takaddama ta zaben fidda gwani a APC za ta karkare, inda kowanne daga bangare biyu ke kan bakar sa ta ko a yi na sa zabi ko a ce nadi kawai za a yi.

Saurari Rahoton Nasiru Elhikaya domin karin bayani....

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Ci Gaba Da Sa In Sa Kan 'Yar Tinke A Jam'iyyar APC- 2'59"