Ana Ci Gaba Da Korafi Kan Nade-naden Shugaba Buhari

Shugaba Muhammad Buhari

Ana ci gaba da cece-ku-ce akan nada Ahmed Rufai Abubakar a matsayin shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA.

Jama'a a Najeriya na ci gaba da tsokaci kan nadin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi wa Ahmed Rufa'i Abubakar a matsayin shugaban hukumar tattara bayanan sirri.

A cewar Ja'afar Ja'afar, babban editan jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian, nadin Abubakar bai dace ba, lura da cewa shi ma daga Jihar Katsaina ya fito.

A cewar Ja'afar wannan abu ne da bai dace ba kuma yana da hadarin gaske saboda bai cancanta ba.

Nadin na Abubakar a matsayin shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA, na ci gaba da shan suka hatta daga bangaren masu goyon bayan shugaba Buhari.

"Gwamnatin da take gadara da maganar tabbatar da gaskiya an samu mutumin da ya fadi jarabawar zama darakta sau biyu ka daukoshi ka nadashi" Inji Isa Tijjani, wani mai goyon bayan Buhari.

Sai dai Ministan wasa da kula da matasa, Barrister Solomon Dalung, ya ce an taba yin hakan a lokacin Shugaba Obasanjo.

Saurari karin Dalung a wannan rahoto na Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Ci Gaba Da Korafi Kan Nade-naden Shugaba Buhari- 2' 52"