Jihar Nasarawa da ke makwabtaka da jihohin Benue, Kogi da babban birnin tarayya Abuja na fuskantar matsalolin rashin jituwa tsakanin kabilu, fadan makiyaya da manoma, farmakin ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
Gwamna Sule ya ce sun gana da masu ruwa da tsaki don samar da tsaro a jihar ya kuma ce ranar Laraba 12 ga watan Agusta za a bude wata cibiyar tsaro ta ‘yan sanda da aka kafa a wani wuri da ake yawan yin fashi da garkuwa da mutane a kauyen Endehu na Karamar hukumar Nasarawa Eggon, bayan haka an kuma baza jami’an tsaro
Mai martaba sarkin Nasarawa, Alhaji Ibrahim Usman Jibrin ya ce hakkin tsaro na kowa ne kuma a matsayinsu na iyayen kasa da masu kishin kasa, suna taimaka wa jami’an tsaro da bayanai don dakile kai hare-hare.
A bangare guda, sakataren jam’iyyar APC a jihar Nasarawa Alhaji Aliyu Bello, ya ce yanzu idan aka kama wani mai babban laifi, zai nemi a kai shi kotu saboda ya san idan ya je kotu za a bada belinsa. A saboda haka, ya kamata a sake duba tsarin shari’ar kasar a yi masa garambawul a kuma samar da kotuna na musamman da za su iya zartar da hukunci cikin sauri.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5