Masarautar Doma da ke jihar Nasarawa ta bukaci al’umma ta taimaka wajen bai wa dakarun Najeriya bayanai da zasu kai ga kakkabe bata gari da samar da zaman lafiya a Najeriya.
A ranar Litinin ne Shelkwatar dakarun Najeriya ta kaddamar da tubalin gina wata shelkwata ta musamman a karamar hukumar Doma, jihar Nasarawa, wadda za ta samar da tsaro, musamman a yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya da ke fama da ayyukan bata gari.
Mai Martaba, Andoma na Doma a jihar, Alhaji Ahamadu Aliyu Kauga, ya bukaci jama’a su bai wa dakarun sahihan bayanai da za su taimaka a kokarin da ake na ganin an samar da dawamammen zaman lafiya.
Shugaban kungiyar matasan Fulani ta Miyetti Allah a Jihar Nasarawa, Alhaji Bello Dauga Inusa, ya ce kasancewar rundunar zai kawo karshen tashin hankalin da suke fuskanta.
Shugaban kungiyar matasan Tivi a Jihar Nasarawa, Peter Ahemba ya ce zasu ba dakarun goyon baya a wannan kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti daga Zainab Babaji:
Facebook Forum