Ana can ana ci gaba da kidaya kuri’u a Ghana da ke yankin yammacin Afirka bayan babban zaben da kasar ta gudanar a ranar Litinin.
WASHINGTON D.C. —
Rahotanni na nuni da cewa, ana kusan kankankan tsakanin shugaba mai ci Nana Akufor-Addo na jam’iyyar New Patriotic Party da kuma abokin hamayyarsa John Mahama na jam’iyyar National Democratic Party.
Wannan takara ita ce ta uku da abokanan hamayyar biyu ke yi domin neman kujerar shugabancin kasar.
‘Yan kasar ta Ghana dai sun yi zaben shugaban kasar ne, wanda ke da ‘yan takara 12 da kuma na ‘yan majalisar dokoki da ke da kujeru 275.
Daga cikin muhimman batutuwa da masu zaben suka fi mayar da hankali akai wajen yin, akwai batun ilimi, kiwon lafiya, rashin aikin yi da kuma karancin ababan more rayuwa.
Hukumomin zabe na fatan ganin sun fitar da sakamakon nan da zuwa yammaci ko daren yau Talata.