A yayin ziyarar da wata tawagar jam’ian gwamnatin kasar Indonesia ta kai Jamhuriyar Nijar karkashin jagoranacin karamin mnistan harakokin wajen Indoneiya a makon jiya aka rattaba hannu a yarjejeniyar tsakanin darekatan fadar shugaban kasa Ouhoumoudou Mahamadou da shugaban kamfanin WIKA, na aikin yiwa fadar shugaban kasar kwaskwarima bisa ga cewar jaridar LE SAHEL mallakar gwamnatin nijer koda yake ba ta yi bayani akan kudaden da wadanan aiyuka ke bukata ba…
Kawo yanzu gwamnatin ta Nijer ba ta yi bayani ba dangane da adadin kudaden da wannan kwagila za ta lakume to amma ‘yan adawa na cewa miliyan 14000 na cfa ne za a kashe domin ayyukan kwaskwarimar fadar ta shugaban kasa, abinda Annabo Soumaila shugaban jam’iyar MDN Kokari ta kawanen FDR yace bai dafe ba a daidai lokacin da matsalolin suka addabi talakawa .
Kakakin gwamnatin Nijer Abdourahman Zakari wanda Sashen Hausa ya tuntuba ta wayar tarho ya nemi a bashi lokaci ya sanarda jami’in dake gaban wannan aiki wato shugaban da’irar Yamai Moctar Mamoudou idan ya so daga bisani zai waiwayemu domin zantawa akan wannan batu dake ci gaba da shan suka a wajen ‘yan adawa.
A ci gaba da neman hanyoyin jin ta bakin masu mulki mun tuntubi wani jami’in hulda da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa Adamu Manzo shi ma ya bukaci mu ba shi lokaci domin samun izini daga magabatansa.
Fadar shugaban kasar Nijer na daga cikin gine ginen da gwamnatocin da suka mulki wannan kasa a can baya suka gada daga gwamnatin Gen Seini Kountche bayan kifarda gwamnatin farar hula ta Diori Hamani a shekarar 1974 abinda ake ganin zai iya zama hujja ga gwamnatin Issouhou Mahamadou wajen aiwatar da kwaskwarimar da za ta bayarda huskar zamani ga wadanan gidaje da wasu ke kallon sun zama tsohon yayi.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma
Your browser doesn’t support HTML5