Irin wannan rana ita yau akan gudanar da bukukuwa da taruka a duk fadin duniya musamman a manyan birane inda ake gabatar da kasidu da wasan kwaikwayo tare da tattauna abubuwan da suka shafi rayuwar matan.
Tun a jajiberen wannan ranar ce wasu mata a jihar Borno suka soma nasu bukukuwan da bayyana matsalolinsu da kuma neman maslaha ganin cewa a jihar Borno mata da dama suka samu matsala musamman ma matan da aka kashe mazajensu sakamakon rikicin kungiyar Boko Haram.
Kawo yanzu an yi kiyasin cewa mata fiye da dubu 50 ne suka rasa mazajensu a jihar Borno kawai.
Akwai kuma wasu da aka sace mazajensu har yanzu ba'a san inda suke ba.
Hon. Fanta Baba Shehu, shugaba ce a ma'aikatar harkokin mata a jihar Borno, ta kuma ce yanzu abun da suka sa gaba shi ne ilimin yara kanana da kuma ba mata ilimin yaki da jahilci. Abu na biyu shi ne tanadawa matan jari domin su samu abun dogaro da kai.
Shugabar kungiyoyin matan jihar Borno ta ce kawo yanzu suna da kungiyoyi na mata zalla fiye da dubu biyar a jihar da kuma suka yi rajista a karkashin kungiyarta.
Matan da aka zanta dasu sun ce suna bikin ranar tunawa da mata da farin ciki amma kuma da bakin ciki a wani gefen saboda wasu cikinsu da suka rasa mazajensu.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5