Ana Bukatar Taimakon Gaggawa A Bahamas

Bayan da mahaukaciyar guguwar nan mai hade da ruwa da iska da aka yiwa lakabi da "Dorian" ta lalata tsibirin Bahamas, yanzu haka ana neman taimakan gaggawa ga mutanan tsibirin.

Saboda munin barnar da mahaukaciyar guguwar nan ta Dorian ta yi a Bahamas, har ‘yan kasar sun fara rasa yadda za su bayyana al’amarin.

An yi ta amfani da kalmomi irinsu, “karshen duniya,” da “kaduwa,” da “tamkar tashin bam” da dai sauransu wajen bayyana al’amarin, to amma kusan kowace kalma gani ake ba ta da karfin bayyana halin da ake ciki a wurare irinsu tsibirin Abaco da tsibirin Grand Bahama.

Guguwar ta Dorian ta kwashe kusan kwanaki biyu ta na ta yamutsa arewacin tsibiran na Bahamas da ruwa kamar da bakin kwarya da iska mai dira da matukar karfi da ke kadawa da gudun kilomita 251 a sa’a guda.