Ana Bukatar Magance Yunwa Da Gaggawa A Arewa Maso Gabashin Afirka - MDD

Mark Lowcock

A yau Laraba shugaban hukumar da ke kula da harkokin ba da agaji na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce akwai bukatar kudade na gaggawa don a magance yunwa a yankin arewa maso gabashin nahiyar Afrika bayan da aka kara samun karancin ruwan sama.

Mark Lowcock ya ce zai saki dala miliyan 45 daga asusun gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya don taimakawa a Somalia, Ethiopia da Kenya.

Amma ya ce ana bukatar karin kimanin dala miliyan 700 a wannan shekara don hana matsalar yunwa kamar wacce ta faru a Somalia a shekarar 2011, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum dubu 250.

Daga cikin kudade da aka rarraba, dala miliyan 30 na Somaliya ne, dala miliyan 10 ga Ethiopia da dala miliyan 5 na Kenya.

"Na fi damuwa da Somalia, inda a karshen shekara, muna tunanin akwai mutane miliyan 5.4 da ke fama da mummunan rashi, miliyan 2.2 na iya kasancewa cikin mummunar yanayi," a cewar Lowcock yayin da yake ganawa da wani karamin rukuni na manema labarai.