Ana Alakanta Eden Hazar Da Maye Gurbin Cristiano Ronaldo A Real Madrid

Dan wasan Chelsea, Eden Hazard ya ce "ba zai bar" kulob din ba yayin da ake kokarin kammala saye da sayarwa na ‘yan wasan kwallon kafa a Nahiyar Turai a ranar 31 ga Agusta.

Ana alakanta dan wasan da komawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid domin maye gurbin Cristiano Ronaldo. Manchester United ba tayi abun da ya dace ba a gasar Firimiya ta Ingila tsakanita da Brighton, in ji kyaftin dinta Paul Pogba, "Na sanya kaina na farko, ta halin da nake ciki ba daidai ba ne. Za mu ci gaba da ƙokari kuma darasi ne a gare mu”. A cewar sa.

Shi kuwa a nasa bangaren, Kocin kungiyar Mourinho ya ce ba zai zargi kowa ba, duk da cewa ya amincewa da ya yi kuskure "Mun yi kuskure a wasu lokutan da muka samu dama mai mahimmanci a yayin wasan”.

Ku Duba Wannan Ma Wasu Daga Cikin Zaratan 'Yan Wasan Da Kungiyoyi Ke Gab Da Kammala Saye

Manchester City, na son karawa dan wasan bayanta John Stones, albashi na fam dubu £120,000. duk sati domin cigaba da Yarjejeniya da dan wasan mai shekaru 24 da haihuwa har zuwa 2022.

Dan wasan Chelsea Ruben Loftus-Cheek, mai shekaru 22, a duniya zai yi magana da jami'an kulob din a wannan makon game da makomarsa. Dan wasan zai nemi damar tafiya wata kungiya a matsayin aro idan Kocin kungiyar Maurizio Sarri, ba zai iya bashi cikiken lokaci na samun wasanni ba.

Mai tsaron Raga na Manchester United, David de Gea, mai shekaru 27, da haihuwa yana kusa da sanya hannu a sabuwar yarjejeniyar kwantiragi inda zai ki karbar fan dubu dari 200 duk sati a matsayin albashi a Old Trafford.

Dan wasan Chelsea da Spain Alvaro Morata, mai shekaru 25, da haihuwa ya ce "babu wani tunanin zai bar kulob din a wannan lokacin rani, duk da la'akari da makomarsa a kulob din.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Alakanta Eden Hazar Da Maye Gurbin Cristiano Ronaldo Real Madrid