Hukumar ‘yansanda tare da hadin kan bankin samar da gidaje na tarayya ne suka gina gidajen wadanda aka bada su rance kan naira miliya biyar kowannensu da zasu biya a cikin shekaru talati.
Wasu daga ckin ‘yansandan da suka ci gajiyar shirin sun ce samar da gidajen ya kauda fargabar da suke da shi na matsalar mallakar gida bayan sun yi ritaya. Lamarin da ya sa wasunsu sun ci gaba da zama a barikoki bayan sun yi ritaya.
Kwamishinan ‘yansanda na jihar Adamawa Mal. Mohammed Ghazali wanda ya wakilci babban sifeton ya fada a hirar da yayi da Muryar Amurka cewa matakin na zuwa ne sakamakon la’akari da irin wahalhalun adadin, an ware kashi saba’in na gidajen wa kananan jami’an ‘yan sanda yayin da ragowar kashi talatin za a baiwa farar hula.
Matakin da shugaban kwamitin kyautata hulda sakanin ‘yan sanda da farar hula na jihar Adamawa Alh. Abubakar Sahabo Magaji ya ce zai kara dankon zumunci da rage kyamar da jama’a suke yi wa ‘yan sanda.
Shi ma jami’in bankin samarwa masu karamin karfi gidaje na tarayya dake jihar Adamawa Mal. Baba Mohammed ya yi bayanin cewa duk wani ma’aikaci da yake ajiye kashi biyu bisa dari na uwar albashinsa ya cancanci cin gajiyar shirin.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5