Yawancin masu zanga zangar sun fito ne daga yankin kudancin Borno da 'yan gudun hijira dake zaune a Abuja.
An gansu kuma dauke da kwalaye dake nuna kin jinin shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki da Sanata Dino Melaye.
Wani daga kudancin Borno wanda ya fito daga karamar hukumar Gwoza ya ce su ne suka zabe shi suka tura shi Majalisar, saboda haka su ne ya kamata su janye shi.
Masu zanga zangar sun kuma sun gamsu da wakilicin da yake masu.
A makon da ya gabata Majalisar ta dakatar da Sanata Ndume bisa abin da suka kira cewa ya kunyata majalisar a idon duniya yayin wani jawabi da ya yi.
Wata daga cikin masu zanga zangar mai suna Liatu Ayuba, ta yi kira ga Majalisar cikin da ta mayar masu da wakilinsu cikin gaggawa.
To sai dai Majlisar ta tura Sanata Binta Mashi Garba wurin masu zanga zangar da albishirin cewa za ta duba batun dakatar da Sanata Ndume domin a cimma matsaya.
Sanya bakin gwamnan Borno Kashim Shettima da wasu dattawa suka yi ya yi tasiri wajen sassauta matsayin Majalisar wadda a baya ta dauki matakin ba sani ba sabo.
Gabanin wannan zanga zanga, a wata hira ta musamman da yi ya da Muryar Amurka, Sanata Ndume, ya ce shi ba ga laifin da ya yi ba.
"A bisa sani na ni ban yi wani laifi ba." In ji Sanata Ndume, ya na mai cewa bai yi da na sani ba maganar da ya yi wacce masu lura da al'amura suka ce ita ta harzuka 'yan Majalisar.
Domin jin karin bayani saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5