Zanga-zangar ta lumana ta kumshi dukkan shugabannin jam’iyyar na matakin kananan hukumomi da mazabu, da ma sauran ‘yan jam’iyyar daga sassan jihar daban-daban.
Masu zanga zangar sun soma da zagaya titunan Gusau babban birnin jihar, kafin su karkare a shelkwatar jam’iyyar, inda suka gabatar da korafinsu, ta bakin shugaban dandalin shugabannin ja’iyyar na kananan hukumomi, kuma shugaban jam’iyyar na karamar hukumar mulkin Maru, Aminu Abdullahi Gama-Giwa.
Zanga-zangar ta kuma hada har da wasu mukarraban gwamnati kamar kwamishinoni da masu bada shawara na musamman na gwamnan jihar.
Sai dai mataimakin shugaban majalisar karamar hukumar mulki ta Zurmi, Abubakar Daura yace ba dukkan ‘yan jam’iyyar ta APC a jihar ne suka yi zanga-zangar ba.
Wannan lamarin dai ya biyo bayan takaddamar zaben fidda gwani na jam’iyyar ta APC wanda bai yiwu ba, duk da yake bangaren gwamnatin jihar sun ce sun gudanar da zaben, to amma kuma uwar jam’iyyar a karkashin Adams Oshimhole, tayi watsi da shi.
Saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna
Your browser doesn’t support HTML5