An Yi Zanga Zangar Adawa Da Shirin Zabe A Gabashin Ukraine

Dubban masu zanga zanga na gudanar da tattaki a Kyiv babban birnin kasar Ukraine, don nuna rashin amincewarsu da shirin Shugaba Volodymyr Zelenskiy na shirya zabe a yankin gabashin Ukraine da yake karkashin ikon ‘yan aware masu samun goyon bayan Rasha.

A lokacin da su ke gangamin, masu zanga zangar sun yi Allah wadai da shirin zaben da cewa mika wuya ne ga Rasha.

A ranar daya ga watan Oktoba ne, Ukraine, da Rasha da kuma masu shiga tsakani, su Jamus da Faransa, su ka sa hannun akan wata yarjjejeniya tare da ‘yan awaren akan tsarin da za a bi wajen gudanar da zaben a gabashin Ukraine.

Zeleskiy ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wajiba kuma mataki na biye na shirin gudanar da taro tare da shugabannin Rasha, Jamus, da kuma Faransa don a kulla yarjejeniyar zaman lafiya.