Mazauna yankin Mathare na Nairobi sun yi tattaki a jiya Litinin don yin zanga zangar nuna rashin jin dadi cinzalin da ‘yan sanda suke yi yayin aiwatar da dokar hana fita a wani bangare na dakile yaduwar cutar COVID-19.
Hukumar da ke saka ido kan harkokin ‘yan sanda a Kenya mai zaman kanta ta IPOA ta samu korafe-korafen zargin kashe mutum 15 da ake alakantawa da ‘yan sandan.
Hakan na faruwa ne tun lokacin da aka saka dokar hana fita daga yamma zuwa wayewar gari da ta fara aiki a karshen watan Maris.
Hukumar ta ce tana kan gudanar da bincike kan wadannan korafe-korafe.
Hakazalika kungiyoyin kare hakkin dan adam sun dora alhakin mutuwar mutum 20 sanadiyyar aiwatar da dokar hana zirga zirga da aka saka.
Zanga zangar ta ranar Litinin ta gudana ne a ciki da kewaye na yankunan da suke da cunkoso.