An sami wata mummunar zaizayar kasa a kasa a kasar Sin har ta hallaka wasu mutane tare da jikkata wasu.
WASHINGTON DC —
Kafar yada labaran kasar Sin ta bayyana cewa, wata babbar zaftarewar doron kasa ya binne wasu gine-gine akalla guda 22 da rukunin gidajen ma’aikata guda 2. Mutane 21 sun bace, amma rahoton baya ya nuna mutane 41 ne suka bata.
Kamfanin dillancin labaran China na Xinhua (Shinhuwa) yace, zaftarewar kasar ta faru ne a Shenzhen (Shenzen) dake lardin Guangdong (Guwondon) da safiyar lahadin nan. An kuma tura daruruwan masu aikin ceto zuwa wajen.
Jami’ai sun ce an ceci mutane 4 daga masifar wadanda 4 daga cikin su suka dan ji rauni. Yankin Shinhuwa bai fadi adadin rasa rai ko jikkata ba har yanzu.
Sannan ba tabbacin abinda ya haddasa zafatarar kasar da ake yawan samu a ‘yan shekarun nan.