Yekuwan nemarwa kananan hukumomi ‘yanci yana da dumbin tarihi a Najeriya, tun daga zamanin taron kasa na Vision 2010 zamanin mulkin marigayi Sani Abacha da aka gudanar a shekarar alib da dari tara da saba’in da bakwai da taron kasa na gwamnatin Olusegun Obasanjo, a shekarar dubu biyu da biyar, da na gwamnatin Goodluck Jonathan a shekarar dubu biyu da goma sha hudu, da kuma sake tsarin kundin tsarin mulkin kasa da majalisar dokokin tarayya tayi karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattijai Ike Ikweremadu. Da kuma tarruruka da yekuwa daga kungiyoyi da dama.
Daruruwan malamai da suka yi zanga zangar sun zaga birnin tarayya Abuja, dauke da kwalaye dake nuna goyon bayansu, game da ‘yancin kananan hukumomi, amma suka ce a kyale hidimarsu ta ci gaba da kasancewa karkashin jihohi.
Masu zanga zangar sun bayyana takaicin ganin hukumomin jihohin suna karkatar da albashin ma’aikatan kananan hukumomi da ake basu zuwa gudanar da wadansu ayyuka na dabam. Bisa ga cewarsu, kasancewa mulki yana hannun gwamnoni, basu damu su kori malamai ba.
Masu zanga zangar sun yi kira da a cire harkar malamai daga karkashin ikon gwamnatin jihohi idan ana son ci gaban ilimi a wannan matakin.
Shugaban hadaddiyar kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi na kasa, Ibrahim Khalil ya bayyana yadda yunkurin malaman zai shafi ‘yanci kananan hukumomi. Bisa ga cewarsa, tun farko sun zauna sun cimma yarjejeniya da malaman makarantun firamare na kananan hukumomi inda suka bukaci a cire batun albashin malaman daga karkashin kananan hukumomi, amma daga baya, domin neman yin babakere, sai gwamnoni suka kara hankada albashin kananan hukumomin zuwa karkashin gwamnatocin jihohi.
Ga cikakken rahoton da wakiliyarmu Madina Dauda ta aiko mana daga birnin tarayya Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5