Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Dakatar Da Shugabannin Makarantun Firamare 9


Biyo bayan zanga-zangar lumana da dalibai tare da malaman makarantun firamare na jihar Taraba suka gudunar don neman a biyasu albashinsu na kusan watanni takwas, yanzu haka gwamnatin jihar Taraba ta rubuta takardar dakatar da wasu shugabanin makarantun firamare a jihar.

Kamar yadda bayanai ke nunawa gwamnan jihar Taraban Akitet Darius Dickson Isiyaku, ne ya baiwa shugaban Hukumar Kula Da Makarantun Firamari Na Jihar Taraba, umarnin dakatar da shugabanin makarantun firamare tara wato suspension ,dake fadar jihar sakamakon zanga-zangar lumana da dalibai tare da malamansu suka gudunar don neman a biyasu albashinsu na kusan watanni takwas.

A wata takardar umarni daga hukumar ilimin bai daya da aka aikewa sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jihar 16, an bayyana cewa an dau wannan mataki ne sakamakon zanga-zangar lumana da daliban makarantun firamarr da kuma malaman suka yi, wanda hakan ya sabawa doka.

Hon.Semon Audu Galadima, dake cikin kwamishinonin hukumar kula da makarantun firamare na jihar yace dole gwamnati ta dau wannan mataki.

Tuni wannan batu ya soma jawo cece-kuce, inda wasu malaman ke cewa ai tura ce ta soma kaiwa ga bango, da hakan yasa Malaman da kuma daliban makarantun firamaren nuna fushinsu.

Duk dai yi kokarin ji daga bakin shugabanin kungiyar Malamai NUT, reshen jihar Taraban to amma haka ta bata cimma ruwa ba, domin ko da na tuntube shi ta waya, shugaban kungiyar Malaman jihar Comrade Aliyu Jauro Mafindi, yace suna wani taron gaggawa to amma har lokacin hada wannan rahoto ba’a ji daga gare shi ba.

Barr.M.B Mustafa na cikin lauyoyin da ke kai gwauro da mari don ganin an biya Malaman hakkokinsu yace da ban mamaki wannan mataki da gwamnatin jihar ke shirin dauka a yanzu.

Ga rahoton da Ibrahim Abdul’aziz ya aiko mana

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG